ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, kafofin yada labaran kasar ta Sudan sun sanar da cewa, gwamnan jihar Port Sudan Abdullah Chingarai Auhaj ya bayar da umarnin kafa dokar ta-baci a wasu bangarori na jihar, sakamakon rikicin kabilanci da ya barke, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 5, tare da jikkatar wasu.
Bayanin ya ce gwamna Abdullah ya bayar da wannan umarni ne domin kauce wa yaduwar rikicin zuwa sauran yankuna na jihar, daga cikin yankunan da dokar ta shafa dai akwai Dimun Nur, Qadisiyya, da kuma Ummul Kura.
Kamfanin dillancin labaran kasar Sudan ya bayar da rahoton cewa, rikicin wanda na kabilanci ne zalla, ya yi ajalin akalla mutane 5, tare da jikkatar wasu 13, kuma tuni jami’an tsaro suka shiga sintiri a wadannan yankuna, domin tabbatar da doka da oda.
342/